Gwamnatin Kano Ta Samar Da Baburan Ban-ruwa Ga Bishiyoyin Kan Titi
Gwamnatin Kano Ta Samar Da Baburan Ban-ruwa Ga Bishiyoyin Kan Titi
Gwamnatin jihar Kano ta samar da wasu babura masu zubar da ruwa don yin ban-ruwa ga bishiyoyin da aka shuka don ƙawata titunan birnin jihar da kuma damar da yanayi da iska lafiyayya a jihar.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya baiyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce baburan na zamani ne da aka samar da su don kare shi ko kin daga lalacewa.
A cewar Dakta Hashim, ma'aikatar sa na karɓar ƙorafe-ƙorafe na yadda aka fara lalata shukokin da kuma barin dabbobi su na cinye wa, lamarin da ya sanya ya kai ziyarar gani-da-ido don daukar matakin da ya dace.
"Biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe da al’ummar Jihar Kano suka gabatar mana, a yau mun kai ziyara gani-da-ido zuwa wasu daga cikin wuraren da muke aikin ƙawata tituna da shuke-shuke, a inda muka duba halin da suke ciki, tare da kafa matakan da suka dace domin tabbatar da ingancin lafiyarsu," .
Hashim ya tabbatar wa da al'ummar Kano cewa ma'aikatar sa ba za ta bari shuke-shuken su lalace ba.
"Ina tabbatar wa jama’ar Kano cewar ba za mu bari waɗannan shuke-shuken su lalace ba saboda ƙarancin ruwa, kamuwa da cututtuka ko kuma ɓarna daga dabbobi ko mutane ba.
" A halin yanzu, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samar da mashinan ban-ruwa na zamani da za'a riƙa amfani dasu wurin bawa bishiyoyin ruwa a faɗin jihar. Haka kuma muna ɗaukar matakan tabbatar da kariya da dorewar wannan shirin mai muhimmanci tare da tabbatar da kyakkyawan yanayi a jihar Kano baki ɗaya.