Maisanda Yayi Kira ga Matasa Su Rungumi Ilimi Da Sana’a, Ya Bayyana Hasashen da Ya Yi Kan Amurka, Iran Da Jihohin Najeriya
Maisanda Yayi Kira ga Matasa Su Rungumi Ilimi Da Sana’a, Ya Bayyana Hasashen da Ya Yi Kan Amurka, Iran Da Jihohin Najeriya
Shahararren malamin taurari a Jihar Sokoto, Malam Abubakar Maisanda, ya yi kira ga matasan Najeriya da su tashi tsaye wajen neman ilimi da sana’a domin dogaro da kansu.
Maisanda ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilin jaridar _The Path_. _“Matasa su tashi tsaye wajen neman ilimi da kuma sana’a domin dogaro da kai,”_ in ji shi. Ya jaddada cewa ilimi ne mafita ga matsalolin kai da na ƙasa.
Tarihi da gwaninta:
Maisanda ƙwararre ne a fannin taurari. Ya ce ya gaji wannan aiki daga wajen mahaifinsa, wanda shi ma malami ne. Ya shiga fannin ne don _“tafiya da zamani”_.
Ya ce shekara 3 kenan da fara fitowa a kafafen yaɗa labarai, amma ya kwashe shekara 20 yana cikin wannan harka. A wajen neman ilimi, ya ce ya yi yawo har ƙasar Mali da Agadez.
_“Ba wai ina yin wannan bincike ba ne don wata manufa ko cin zarafi ba. Yanayi ne na ra’ayin kaina,”_ in ji shi.
Hasashen da ya yi a Najeriya:
Maisanda ya ce daga cikin bincikensa na farko akwai:
1. Matsalar da aka samu da Sarki Sanusi.
2. Saɓanin Abba Gida-Gida da Kwankwaso, da rushe-rushen gida da annobar da ta biyo baya.
3. Batun Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi da ya ce EFCC za ta kama shi.
4. Baƙin da aka kama a Jihar Filato da ake zargi da taimakon ’yan ta’adda. Ya ce ya faɗa cewa gwamnati za ta kama shi ta kore shi.
5. Hasashen da ya yi kan Jihar Gombe kan abubuwan da za su faru.
Ya ce duk waɗannan bayanai suna nan a shafinsa na Facebook mai suna _Sheikh Abubakar Maisanda Sokoto.
Sai Kuma Hasashen ƙasashen waje:
1. Amurka:
Ya ce shekara 1 zuwa 2 kafin faruwar lamarin, ya yi binciken da ya nuna saura kwanaki 50 a yi mummunar gobara. Wannan gobara ta faru a Jihar California. Ya kuma ce a lokacin rantsar da shugaban ƙasar, ya lissafa abubuwa 12 da za su faru a mulkinsa, ciki har da zanga-zangar da aka yi masa.
2. Iran:
Ya yi hasashen cewa ƙasar za ta fuskanci ta’addanci, matsalar tattalin arziki, da rashin shugabanci. Ya ce cikin wata uku za ta rasa shugaba. “Cikin ikon Allah, bayan kwana 3 aka samu rasuwar shugaban ƙasar, da kuma kai hari wasu masallatai,”_ in ji Maisanda
Ya bayyana cewa bincikensa ba kai tsaye yake yin shi ba. “Ina yin shi tun wata ɗaya ko sati biyu kafin faruwar abu.”
Littattafai da ɗalibai:
Maisanda ya ce yana da ɗalibai da ke karatu a wurinsa. Ya kuma rubuta littattafai kusan 20 kan harkar taurari. _“Alhamdulillah, littattafaina suna shiga duniya baki ɗaya, irin su Masar da Ghana da ko’ina,”_ in ji shi. Ya ce baiwa ce daga Allah.
Kira da addu’a:
Ya sake jaddada kiran ga matasa: “Su tashi tsaye su nemi sana’a kuma su nemi ilimi, domin ɗaya ba ya samuwa sai da ɗayan.”
Ya roƙi Allah ya ba ƙasar nan zaman lafiya, ya kuma ƙara wa shugabanni ikon yi wa al’umma adalci.
Ya yi kira ga al’umma da su ba shugabanni goyon baya domin samun nasarorin da za su amfanar da kowa baki ɗaya. Daga ƙarshe ya yi addu’a: _“Allah ya kawo wa ƙasar mu zaman lafiya mai ɗorewa.”